Hadiza Gabon Ta shigar da Karar Wani Kan Zargin Bata Mata suna
Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, ta maka wani Bala Musa, ma’aikacin gwamnati, a gaban wata kotun Majistare da ke zamanta a Titin Daura, a jihar Kaduna bisa zargin ɓata mata suna.
Jarumar, wacce ta shigar da ƙarar ta hannun lauyanta, Mubarak Sani, ta ce ta fuskanci munanan kalamai da kuma cin mutuncin daga jama’a saboda sharrin da wanda ake kara ya yi mata.
Ya kara da cewa, mutane musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo sun kira Gabon da macuciya, wacce ta riƙa cin kuɗaɗen Musa ta kuma ƙi auren sa, zargin da aka tabbatar da cewa karya ne.
Wanda ake tuhumar, ta bakin lauyansa, Naira Murtala, ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi lauyan mai karar ko suna da shaidu, inda su ka amsa da cewa suna da su.
Alkalin kotun ya bayar da belin wanda ake kara da sharadin ya gabatar da wasu amintattun mutane biyu mazauna jihar Kaduna kuma dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati.
Ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin mai karar ya gabatar da shaidu.