Video Jarumin Kannywood Abdul M Sharif Zai Auri Jaruma Maryam Malika

ƘARSHEN tika-tika, tik! Jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef, wanda aka fi sani da Abdul M. Shareef, da Maryam Muhammad Ƙaura, wadda aka fi sani da Maryam Malika, za su yi aure bayan doguwar soyayyar da suka sharɓa.
Za a Daura auren nasu ne a ranar ranar Juma’a 27 ga watan July 2025, a masallacin Alhaji Sani Zangon daura dake yan kaji hanyar Kaduna zuwa zaria da musalin Karfe 1.00 na rana
Mujallar Film Ta Ruwaito cewa Maryam Malika ta taɓa yin aure sannan tana ƴaya
Tun Bayan fitowar Maryam Malika daga gidan miji Soyayya mai karfi ta kullu tsakaninta da jarumi Abdul M Sharif
A yanzu malika zata shiga gidan Abdul M Sharif nan da sati biyu
Allah Ya Sanya Alkairi Ya Basu Zaman Lafiya
Ga video Wakar Maryam Malika Tare Da Abdul M Sharif
