Uncategorized

Hukumar Tace Finafinai Ta Jahar Kano ta haramta Kauyawa Day

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da haramta bukukuwan Kauyawa da ake yi a faɗin jihar, a wani mataki na ƙarfafa kyawawan ɗabi’u tsakanin al’umma da kuma bin doka.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai a yau Asabar, inda ya ce an kuma dakatar da dukkan wuraren gudanar da bukukuwan wato ‘event centers’ har sai abin da hali ya yi.

El-Mustapha ya ce wannan mataki da suka ɗauka wani ɓangare ne da hukumar ke yi na ƙarfafa ɗabi’u masu kyau tsakanin al’umma.

“Wannan mataki da muka ɗauka yana cikin tsarin dokar hukumar mu wanda majalisar jiha ta yi wa garambawul da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu,” in ji El-Mustapha.

Ya ƙara da cewa dokokin sun bai wa hukumar tace finai-finai ta jihar Kano damar kula da kuma sa ido kan ayyukan da DJ (waɗanda ke saka waƙoƙi a bukukuwa) ke yi da kuma dukkan wuraren bukukuwa a faɗin jihar Kano.

“Daga yau duk wanda ya shirya biki da sunan ranar Ƙauyawa ya aikata laifi,” in ji El-Mustapha.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da jami’an tsaro, ciki har da Hisbah da ƴan bijilanti da su haɗa-kai da hukumar domin tabbatar da cewa an bi wannan mataki na haramta bukukuwan ƙauyawa sau da kafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button