Uncategorized

Topha Wata Kotu A Jahar Kano Ta Turai Kilina Gidan Gyaran Hali

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu a Jihar Kano ta tura Jarumin Kannywood kuma dan TikTok Abubakar Kilina gidan gyaran hali, bisa zargin shigar ‘yan daudu da furta kalamai marasa tarbiyya a bidiyonsa.

Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta shigar da ƙara a kansa, inda lauyan gwamnati Barista Garzali Maigari Bichi ya karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa, kuma nan take Kilina ya amsa.

Alkaliyar kotun majistiri mai lamba 21 da ke No-Man’s-Land, Hajiya Hadiza Muhammad Hassan, ta dage sauraron karar zuwa 17 ga Yuni, 2025, tare da bada umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har zuwa lokacin yanke hukunci.

Hukumar tace fina-finai ta sha jan kunnen matasa kan wallafa abubuwan da suka saba da al’ada da addini a kafafen sada zumunta.

Kalli Sabuwar Wakar Hausa Da ta fito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button