Uncategorized

MashaAllah Mutane 50 Sun Musulunta Sanadiyyar Maryam Shetty

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Mutanen Waɗanda Suke Karatu A Kwalejin Ilimi Ta Zuba Da Ke Birnin Tarayya, Sun Musulunta Ne Biyo Bayan Jawabin Karɓar Ƙaddara Da Su Ka Ji Dakta Shetty Ta Fitar A Shafinta Na Facebook Lokacin Da Aka Cire Sunanta Daga Ministocin Shugaba Tinubu.

Sama da mata 50 sun musulunta a kwalejin ilimi ta Zuba da ke birnin tarayya Abuja sanadiyyar sarauniyar Matasan Arewa, Dakta Maryam Shetty.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito hakan daga shafin Dakta Shettin cikin wani saƙon sanar da ita musuluntar mutanen da aka turo mata daga makarantar. A cikin saƙon an bayyana cewa rungumar ƙaddara da Dakta Maryam ta yi lokacin da aka cire sunanta daga cikin jerin ministocin Nageriya a gwamnatin Tinubu shi ne ya yi silar musuluntarsu.

Kamar yadda su ka ce: “Hajiya Maryam mu na sanar da ke cewa mu na da waɗanda ba musulmai ba sun karɓi musulunci, ko da a yau ma an samu ƙarin wata mace ta musulunta. Mu na da waɗanda su ka musulunta a dalilin Imani da kika nuna na karɓan ƙaddara lokacin da aka cire sunanki a matsayin minista. Ranki ya daɗe idan har kin ba da dama zan gabatar da su a gare ki”. Aka bayyana cikin saƙon.

Saƙon ya cigaba da cewa: “Tuni mun sanya su a makarantar Islamiyya ta (Nusret Educational and cultural limited) da ke Jabi, Abuja. Mun ɗauki nauyin karatunsu da abincinsu. Wasu daga cikinsu suna matuƙar buƙatar ki tallafe su da gudunmawa kamar: Qur’ani, Dardumar Sallah, Jallabiya da Carbi, da sauransu. Mun gode”. Saƙon ya ƙara da cewa.

A nata ɓangaren, ita ma Hajiya Maryam Shetty ta bayyana jindaɗinta gami da godiya ga Allah bisa faruwar wannan al’amari na musuluntar mutane a sanadiyyarta. “Alhamdulillah, daga Allah ne”. Ta ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button