Uncategorized

Dalilin Da Yasa A kori Rahama Sa’idu Daga Makarantar

Kwalejin koyon aikin jinya ta jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi ta musanta korar dalibarta mai suna Rahama Sa’idu bisa dalilin fitowa a kafar TikTok.

Rahama, wata fitacciyar ƴar Tiktok da Instagram ce, wacce a ke ta rade-radin cewa makarantar ta kore ta saboda wallafa bidiyoyi a shafukanta na sada zumunta.

Sai dai kwalejin ta karyata jita-jitar, inda ta ce an kori ɗalibar ne saboda rashin bin ka’idojin kwalejin.

A cewar kwalejin, an kori ɗalibar daga makarantar ne saboda ta fadi jarrabawar da ta yi, kuma ta ki karbar zaɓin maimaitawa kamar yadda dokokin makarantar su ka sharɗanta

Bisa ga dokokin kwalejin, duk dalibin da ya yi sati 3 ba a makaranta ko asibiti ba, ba tare da wani dalili na hakika ba, to zai maimaita wannan zangon karatu kai tsaye.

Rahama Saidu ta fadi jarabawa watanni 5 da suka wuce, tun daga lokacin ne ta daina zuwa makaranta ba tare da wani dalili ba. Ba ta amince da maimaita zangon karatun ba, ta kuma ƙi amsa dukkanin tambayoyi na jin bahasi da aka riƙa aika mata,” wata sanarwa da makarantar ta fitar ta bayyana.

Sanarwar, duk da haka, ta lura cewa kwalejin ba ta san cewa Rahama ‘yar Tiktok ba ce

Saboda haka, duk zarge-zargen da Rahama ta yiwa kwalejin karya ne, maras tushe kuma zargi ne kawai don bata sunan kwalejin wanda ya kamata jama’a su yi watsi da su,” in ji sanarwar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button