Kannywood

Tirkashi Auren Jaruma Hafsat Idris Ya mutu Ta dawo Film

WASU ‘ya’yan masanaantar finafinai ta Kannywood sun bayyana damuwa kan mutuwar aurarraki biyu – na tsofaffin jaruman Kannywood Hafsat Idris da Zahra’u Shata.

A ganin su, mutuwar Auren Hafsat Idris za ta ƙara ƙarfafa ƙaryar da wasu ke yi cewa ‘yan fim mata ba su son zaman aure.

‘Yan Kannywood ɗin sun bayyana damuwar ne lokacin da mujallar Fim ta nemi jin abin da za su iya cewa kan ganowar da ayi cewa auren Jaruma Hafsat Idris Ya mutu inda ta dawo taci gaba da harkar Film

Ba yanzu ba ne aurarrakin waɗannan tsofaffin jaruman su ka mutu, domin kuwa an shafe watanni, to amma kafin wannan lokaci wasu masu lura da al’amuran industiri sun daɗe su na ɗora ayar tambaya kan yadda waɗannan matan su ka buɗe sabuwar mu’amala wadda ta bambanta da yadda su ka riƙa gudanar da rayuwar su a matsayin matan auren a baya.

Kowaccen su ta ƙara himma wajen ɗora saƙwanni a soshiyal midiya, musamman a Instagram da TikTok, sannan an gan su sun tsoma ƙafa cikin harkokin Kannywood.

Ita dai Hafsat Idris, wadda aka fi sani da Hafsat Ɓarauniya, mun ba ku labarin sun yi aure a asirce ne da wani matashi a Kano mai suna Mukhtar Hassan Hadi, a ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022.

Wata makusanciyar jarumar ta ce lamarin mutuwar wannan auren bai mata mamaki ba “saboda aure ne da ake ganin an yi shi na sha’awa da biyan buƙata a ɓangarorin biyu.

Wata makusanciyar jarumar ta ce lamarin mutuwar wannan auren bai mata mamaki ba “saboda aure ne da ake ganin an yi shi na sha’awa da biyan buƙata a ɓangarorin biyu.

Majiyar mu ta ce: “Hafsat ta auri ƙaramin yaro da ta girme shi nesa ba kusa ba, kuma iyayen sa ba su son auren tun da farko. Sun so ta auri sa’ar sa kuma wacce ba ‘yar fim ba.”

Wakilin mu ya samu labarin cewa auren ya mutu ne kusan watanni bakwai da su ka wuce, amma ba a gane ba domin Hafsat ta na zaune ne a gidan ta, ba gidan angon ba. Don haka ba sai an gan ta ta na famar kwashe kaya ba ko canza gida ba.

“Haka kuma ta riƙa shiga cikin dangin sa, har ana yin bukukuwa tare da ita,” inji wata majiyar.

Tuni dai Hafsat ta dawo ruwa cikin harkar fim tsundum, inda a yanzu haka ta na daga cikin jaruman da ake ɗauka a shirin dirama mai dogon zango na furodusa Abdul Amart Mohammed, wato ‘Manyan Mata’.

Kwanan nan an gan ta a wajen ɗaukar fim ɗin a Kaduna, kuma “kai da gani ka san ba ta da aure,” inji wani ɗan wasa wanda ya halarci ɗaukar fim ɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button