News

MashaAllah Ahmad Musa Ya taimaka ma baba Kurkuzu

CAPTIN AHMED MUSA YA AIKEWA ƊAN FIM ƊIN HAUSA BABA KARKUZU TALLAFIN NAIRA 500,000, YA KUMA SA A NEMO KATAFAREN GIDA NA NAIRA MILIYAN 4 ZUWA NAIRA MILIYAN 5 ZAI SAYA MASA

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya, Captin Ahmed Musa MON ya ba da umarnin a Nemo gida wanda kuɗinsa ya kai Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zai sayawa ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu,

sannan kuma a yanzu haka ya aike masa da tallafin kuɗi Naira 500,000 domin ya yi cafane duba da halin ƙunci, matsi, gami tsananin rayuwa da ya ke ciki.

Wannan ya biyo bayan hirar da Baba Karkuzu yayi da tashar Zinariya TV ne. Captin Ahmed Musa ya bayyana cewa “Na yi magana da Baba Karkuzu ta waya, na kuma tabbatar masa na ba shi tallafin Naira 500,000 ya yi cafane.

Bayan haka kuma na shaida masa cewa na ba da umarnin a nemo masa gida na Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zan saya masa daga nan kuma mu ga tayadda zan ƙara taimaka masa”. In ji Ahmed Musa.

A ƴan kwanakin nan ne dai aka jiyo tsohon ɗan wasan Hausan, Baba Karkuzu ya na kokawa kan halin ƙunci da ya ke ciki, tayadda har ta kai ya makance ba ya iya gani saboda ƙuncin rayuwa, har ma wasu ke nema masa tallafi a Social Media domin a taimaka masa.”

Sama da shekaru 43 Ina harkar Fim, amma yanzu sai a wayi gari babu abinda za a ci a gidana. Kuma yanzu haka na daina gani, sannan kuma gidan da na ke ciki mai shi ya saka shi a kasuwa”, Cewar ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu.

Wannan labarin ya taɓa Captin Ahmed Musa sosai ya yi jimamin halin da Baba Karkuzun ya ke ciki, domin tun ya na yaro a birnin Jos ya ke ganin wasannin Baba Karkuzun a gidan talabijin na NTA.

Ganin haka ya sa Captin Ahmed Musa ya nema ya yi magana da shi ta waya ya kuma yi masa wannan albishir da wannan tallafi na gida da kuɗi.Captin Ahmed Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen taimako da jinƙan al’umma, ko da a baya-bayan nan, ya sayawa wasu matasa mutum 4 manya-manyan gidaje a Kano domin su zauna da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button