Kannywood

Shugaban Kasar Nigeriya Bola Ahmad Tunubu Ya Naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Tace Finafinai Na Nigeria

MashaAllah Shugaban Ƙasar Nigeria Bola Ahmad Tunubu Ya Naɗa Shahararren Dan Wasan Hausa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Tace Finafinai Na Nigeria

Naɗin nasa na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a.

Ali Nuhu dai ya yi fice a harkar fina-finai a Kannywood da Nollywood.

Tuni Dai Abokanshi Na Masana’antar Shirya finafinai na Kannywood Su Taya shi murna

Wannan Naɗin dai Ci gaba ne sosai ga Arewacin Najeriya baki ɗaya Domin a Baya ba a taɓa samun Wani ɗan Arewacin Najeriya da ya rike wanna muƙamin ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button